Ministan kudin Nijeriya ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara binciken kwakwaf a kamfanin man fetur na kasa NNPCL.
Da yake jawabi a wurin taron masu saka hannun jari na Najeriya da ke gudana a gefen taron asusun bada lamuni na duniya IMF da Bankin Duniya a birnin Washington na Amurka, Edun ya bayyana cewa sauyin shugabancin kamfanin NNPC na daga cikin matakan tsaftace kamfanin da gwamnatin tarayya ta dauka.
Ministan ya bayyana muhimman sauye-sauye da gwamnatin tarayya ta aiwatar don sake farfado da tattalin arzikin kasar da kuma sanya kwarin gwiwa ga masu zuwa hannun jari.