Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, ta kama tare da tsare wasu masu tallata shafin kudin Crypto na CBEX da ake zargin ya wawure kudaden da suka haura dala biliyan 1 na ‘yan Nijeriya.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ba da umarnin ne, bayan ya saurari bayanai daga lauyar EFCC Fadila Yusuf.
Hukumar ta EFCC ta nemi izinin kotu domin ta kama wadanda ake zargin tallata wannan dandalin tare da tsare su, inda za ta ci gaba da bincike tare da shigar da kara.