Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta kama wasu mutane 27 da suka yi yunkurin zana jarabawar ta 2025 a madadin wasu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dr Fabian Benjamin ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Benjamin ya ce zuwa yanzu an dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin.
Ya kara da cewa hukumar ta kuma rufe wasu cibiyoyi hudu bisa rashin inganci wajen gudanar da jarrabawar a Abuja.