Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa kuma Sakataren Yankin Kudu maso Kudu na jam’iyyar, George Turnah, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a jihar za ta goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 — ko da kuwa Gwamna Douye Diri amince ba.
Turnah, wanda kuma shine jagoran kungiyar New Associates, wata kungiyar dake goyon bayan Nyesom Wike da aka kaddamar a jihar Bayelsa a karshen mako, ya ce mafi yawan gwamnonin Kudu maso Kudu suna marawa Shugaba Tinubu baya ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke ciki ba.
Yayin wani tattakin nuna goyon baya da suka gudanar a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, sakataren na PDP a wannan shiyya ya ce manufar taron shine godewa Shugaba Tinubu bisa yadda ya nada ‘ya ‘yan yankin Neja Delta a manyan mukaman gwamnati.
A cewar Turnah, lokaci yayi da Bayelsa za ta bayyana irin goyon bayan da take da shi domin tabbatar da ci gaba da wakilcin yankin Neja Delta a matakin kasa.