Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya.
Bafarawa, wanda ya kasance jigo a jam’iyyar babbar jam’iyyar adawa ta PDP har zuwa ranar 13 ga Janairun 2025, ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar, yana mai bayyana cewa yana son mayar da hankali kan shirye-shiryen bunkasa matasa.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, tsohon gwamnan jihar Sokoto ya ce ’yan siyasar Najeriya sun fi mayar da hankali ne wajen samun mukaman siyasa ba tare da yin wani abu na amfani ga al’umma ba.
Bafarawa ya yi wannan jawabi ne a yayin da wasu fitattun ’yan adawa ke sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, a shirye-shiryen da ake yi gabanin zaben 2027.