DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yawancin tsofin ‘yan majalissar Nijeriya ba sa iya biyan kudin makarantun ‘ya’yansu – Sanata Bala Ibn Na’Allah

-

Tsohon Sanatan Kebbi ta Kudu, Bala Ibn Na’Allah, ya bayyana cewa da dama daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar dokokin Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki bayan barin kujerarsu, inda har wasu ke kasa biyan kudin makarantar ‘ya’yansu.

Na’Allah ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi da gidan talabijin na Trust TV, inda ya musanta rade-radin da ke cewa shiga siyasa na nufin samun arziki cikin sauƙi.

Google search engine

A cewarsa, “Ka koma cikin al’umma ko mazaba ka duba, ka gaya min wani Sanata ko dan majalisa da bai da wata sana’a kafin siyasa, kuma yanzu da ya bar kujerarsa, ko biyan kudin makarantar ‘ya’yansa yana iya yi?”

Ya bayyana cewa, hoton da mutane ke gani na ƙayatarwa a majalisa ya sha bamban da hakikanin gaskiyar da ke faruwa. Koda yake ya ce bai fito don ya kare ‘yan majalisa ba ne, sai dai yana bayyana abubuwan da ya gani da idonsa a matsayinsa na mai ruwa da tsaki a siyasa.

Na’Allah ya kuma tabo batun yadda wasu ke nacewa kan neman takara ido rufe, inda yace bukatar kaiwa matakin koli a siyasance shine hadafinsu ba zuwa majalisar ba kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An kama wasu ƴan Nijeriya 3 kan zargin aikata damfara ta yanar gizo a Kenya

Rundunar da ke gudanar da binciken manyan laifuka a ƙasar Kenya (DCI) ta tabbatar da kama wasu ’yan Nijeriya uku bisa zargin aikata damfara ta...

BBC ta nemi afuwar Trump kan wani bidiyo da aka fassara jawabinsa ba daidai ba

Shugabancin kafar yada labarai ta BBC ya nemi afuwar shugaban Amurka Donald Trump kan gyaran bidiyon da aka fassara jawabinsa ba daidai ba, tare da...

Mafi Shahara