Dandalin CBEX ya Ci gaba da aiki duk da zargin wawure sama da Naira Tiriliyan 1 na ‘yan Najeriya.
Dandalin zuba jari na CBEX ya koma aiki duk da zargin damfarar sama da Naira tiriliyan 1.2 da ta shafi fiye da ‘yan Nijeriya 600,000.
Wasu masu zuba jari sun tabbatar wa jaridar PUNCH cewa an sake bude dandalin, inda ake baiwa sababbin masu hannu jari damar rajista da kuma cire riba.
Hukuma na ci gaba da bincike don gano ainihin adadin kudin da aka rasa tun bayan rugujewar harkar a watan Afrilu.