Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr Abdullahi Baffa Bichi, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf, inda ya zarge ta da yin almundahana da rashawa fiye da na gwamnatin da ta gabata.
A cikin wani faifan bidiyo, Bichi ya yi ikirarin cewa gwamnati mai ci ta tafka kurakurai fiye da lokacin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda a baya ake zarginsa da cin hanci da rashawa a tsawon mulkinsa na shekaru takwas, a cewar jaridar Dailytrust.
Bichi ya yi nuni da cewa gwamnatin ba za ta kai labari ba a zaben 2027, saboda korafin da ake yi kanta inda ya yi alkawarin fallasa aika-aikar da ake zargin gwamnatin da aikatawa.