Muna zargin hannun wasu a yunkurin bata suna da dagula ayyukan hukumar NAHCON a shirin aikin Hajjin 2025- Musa Iliyasu Kwankwaso
Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa suna zargin ana ƙoƙarin bata suna da dagula ayyukan hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) da shugaban ta, Farfesa Abdullahi Usman.
Hon. Musa Iliyasu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai cewa rahotannin da ke zargin NAHCON da nuna son kai wajen zaɓen ma’aikatan wucin gadi don aikin Hajji na 2025 ba su da tushe.
A ƙarshe, ya bayyana cewa NAHCON na ci gaba da shirye-shiryen Hajjin 2025 ba tare da wata tangarda ba, kuma za a tabbatar da adalci da gaskiya wajen zaɓen ma’aikatan wucin gadi a hukumar.