Shugaban Ć™asa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta lamunci barazana daga cikin gida ko waje ba, yana mai jaddada cewa Ć™asar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro.
Shugaban ya kuma jaddada kudirin gwamatinsa cewa za ta ci gaba da baiwa dakarun kasar goyon baya ta fuskar kayan aiki, bayanan sirri, da kuma tallafin jin daÉ—i, ciki har da gidaje, inshora, da albashi mai tsoka.
Jawabin hakan ya biyo bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Katsina, a daidai lokacin da ake fuskantar Ć™aruwar hare-haren ‘yan ta’adda a jihohin Borno, Filato, da Benue, da Zamfara da sauransu