DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dalibai sama da miliyan 1.5 da suka zana jarabawar JAMB ta 2025 suka kasa cin maki 200

-

Sama da dalibai miliyan 1.5 daga cikin 1,955,069 ne da suka zana jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a shekarar 2025, suka samu kasa da maki 200 a jarrabawar.

 

Wannan bayanin na cikin kididdigar sakamakon na shekarar 2025 da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a JAMB ta fitar ranar Litinin.

Kididdiga ta nuna cewa dalibai 420,415 ne kawai da suka zana jarrabawar suka samu sama da maki 200 a wannan shekarar.

Bayanai sun nuna cewa kashi 75 cikin 100 na wadanda suka zana jarrabwar sun samu maki kasa da 200 a jarrabawar, inda kasa da kashi daya cikin dari suka samu sama da maki 300.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara