Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da sauye-sauyen mukamai a cikin Majalisar Zartaswa ta jiha, a wani yunkuri na inganta aiki da daidaita tsarin mulki.
A cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa:
– Hon. Muhammed Alhassan, da ya kasance Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje, An mayar da shi zuwa Ma’aikatar Ruwa.
– Hon. Ibrahim Garba Hannun Giwa, da yake Kwamishinan Ruwa, yanzu zai jagoranci Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Ci gaban Al’umma.
– Hon. Ahmed Garba (MK), wanda ya ke Kwamishinan Kananan Hukumomi, an tura shi zuwa Ma’aikatar Gidaje, Tsare-Tsaren Birane da Cigaban Yankuna.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wadannan sauye-sauyen sun fara aiki daga wannan Litinin din, 5 ga Mayu, 2025, kuma an umurci dukkan kwamishinonin da su karɓi sabbin ofisoshinsu kafin Litinin, 19 ga Mayu, 2025.