DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin jihar Borno za ta rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri

-

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana shirin rufe sansanin ‘yan gudun hijira da ke Muna a Maiduguri cikin makonni masu zuwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ziyarar da ya kai sansanin ranar Litinin.

Zulum ya ce matakin na daga cikin kudurin gwamnatin jihar na rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira dake Maiduguri da sauran wurare.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa sansanin Muna an kafashi ne biyo bayan tsananin bukatar agaji a jihar kuma a halin yanzu yana dauke da ‘yan gudun hijira kimanin 10,000.

Gwamnan, ya bayyana cewa, aka mayar da kusan kashi 75 cikin dari na ‘yan gudun hijirar zuwa muhallansu, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ba da tallafi don inganta rayuwar sauran ‘yan gudun hijarar yayin da suke shirin komawa gidajensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara