DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar EFCC ta kama wani dan TikTok kan zargin wulakanta takardun Naira a cikin bidiyonsa

-

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC shiyyar Kaduna, sun damke wani matashi Muhammed Kabir Sa’ad bisa zarginsa da wulakanta takardun Naira.

Sa’ad ya wallafa bidiyonsa a shafinsa na TikTok da Instagram inda aka gan shi yana watsi da takardar Naira a kasa tare da tattaka, inda kuma ya kalubalanci jami’an EFCC su kama shi idan za su iya.

A wata sanarwar da ta wallafa a Facebook, hukumar EFCC ta ce an kamo matashin a unguwar Tudun Wada da ke Jihar Kaduna, kuma an kai shi hedkwatar hukumar ta Kaduna domin yi masa tambayoyi.

Hukumar ta ce za a gurfanar da shi gaban kotu idan aka kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara