Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Kafin a fara taron, shugaban kasar ya rantsar da mambobi hukumar dake kula da majalisar dokoki ta kasa karkashin jagorancin Dakta Savior Onyiekere, ya kuma rantsar da sabbin manyan Sakatarori guda biyu.