Shugaba Bola Tinubu zai gana da shugabannin kamfanonin dake samar da wutar lantarki a Nijeriya, a kokarin ganin an biya bashin Naira Tiriliyan 4 da ke barazanar gurgunta hanyoyin samar da wutar lantarki a kasar.
A cewar wata sanarwa da ma’aikatar lantarki ta Nijeriya ta fitar, matakin ya biyo bayan wani taro da aka yi a ranar Talatar da ta gabata tsakanin ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, da shugabannin kamfanonin a Abuja, a dai dai lokacin da ake ci gaba da fargabar yiwuwar rugujewar tsarin samar da wutar lantarkin a Nijeriya.
Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin daukar matakin gaggawa don rage yawan bashin Tiriliyan 4 da ake bi.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kamfanonin sun yi gargadin ga gwamnatin tarayya kan ci gaba da tara bashin da ya haura Tiriliyan 4.