DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Talauci na ci gaba da kassara mutanen karkara a Nijeriya – Bankin Duniya

-

Bankin Duniya ya nuna damuwa kan karuwar talauci a Nijeriya, inda ya ce kashi 75.5 na mazauna karkara suna rayuwa a kangin talauci.

Bankin Duniya ya bayyana hakan ne a cikin sabon rahoto na baya-bayan nan na watan Afrilun 2025.

A cikin wani rahoton da kafar Africa’s Pulse ta fitar, biyo bayan taron asusun ba da lamuni na duniya IMF da bankin duniya da ya gudana a Amurka, ta bayyana da dama daga cikin ‘yan Nijeriya za su fada cikin talauci a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Rahoton na Bankin Duniya ya bayyana mummunan halin da ake ciki na talauci a kasar, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da rashin daidaito tsakanin mazauna karkara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara