DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a fara jigilar maniyyata aikin hajji na Kaduna a ranar 14 ga watan Mayu

-

By Salim Muhammad Ghali

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta fara jigilar maniyata hajjin bana zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 14 ga watan Mayu.

Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin radiyo a yau Talata, inda ya yi bayanin shirye-shiryen da suka yi na gudanar da aikin Hajjin bana.

Kamfanin UMZA Airline ne zai yi jigilar jimillar mahajjata 4,060 na Jihar Kaduna ne ake sa ran za su sauke farali a bana.

Jaridar daily trust ta ruwaito daga cikin matakan da hukumar dauka ta ce dole ne a bi kafin tafiya, an shirya yi wa dukkan mahajjatan binciken lafiya a sansanin mahajjata na Hajj Transit Camp da ke Mando.

Malam Salihu ya ja hankalin dukkan mahajjata da su kiyaye doka da ƙa’idojin da hukumomin Saudiyya suka shimfiɗa, yana mai jaddada muhimmancin ladabi, da biyayya, da kuma kula da lafiya a tsawon lokacin aikin hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara