DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a kashe sama da naira biliyan 750 domin aikin wasu tituna a Nijeriya

-

Majalisar zartaswa ta Nijeriya ta amince da kashe naira biliyan 750 domin yin sabbin tituna da kuma gyara wasu a jihohin kasar.

Ministan ayyuka, Dave Umahi ne ya bayyana haka ga manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Litinin, bayan taron majalisar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.

Umahi ya ce majalisar ta amince da sake yin wasu ayyukan da tsohuwar gwamnatin ba ta kammala ba.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka amince da su har da sake aikin hanyar Akure-Eta-Ogbese-Ekiti zuwa Ikere-Ado-Ekiti, wanda ya ratsa jihohin Ondo da Ekiti.

Kazalika majalisar zartaswar ta sake tantance kwangilolin da aka gada a gwamnatocin baya, ta kuma sake duba aikin hanyar Sokoto-Zamfara-Katsina-Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ba dan NNPP bane tun 2023, in ji shugaban jam’iyyar na kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba. Yayin da...

Sai kun kara damara wajen yaki da matsalar tsaro – Shugaba Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami'an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Shugaba Tinubu ya...

Mafi Shahara