Wata kotu a ƙasar Kenya ta ci tarar wasu mutane hudu sama da dala $7,000 – daidai da kusan miliyan goma a naira – bayan an kama su da yunkurin fasakwaurin dubban tururruwa masu rai daga ƙasar ba bisa ka’ida ba.
Wadanda aka kama sun haɗa da David Lornoy da Seppe Lodewijckx – matasa ‘yan asalin ƙasar Belgium masu shekara 18 kowannensu, tare da Duh Hung Nguyen daga Vietnam, da kuma wani ɗan ƙasar Kenya mai suna Dennis Nganga.
Hukumar Kula da Dabbobi ta Kenya (KWS) ta zargi matasan da laifin ‘bio-piracy’ — wato satar halittu na ƙasa domin kasuwanci ko fasakwauri ba bisa ƙa’ida ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Lornoy da Lodewijckx dauke da kwalabe 2,244 da ke ɗauke da tururruwan sarauniya 5,000, a gundumar Nakuru da ke kusa da birnin Nairobi.
Duh da Nganga kuwa an same su da tururruwa a cikin 140 sirinjin allura da aka cike da auduga da kuma wasu akwati biyu.
Dukkaninsu sun amince da laifin mallakar tururruwan, sai dai sun musanta zargin fasa-kwaurin su zuwa ƙasashen waje.