Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin dakatar da sayar da giya da sauran kayan maye a cikin birnin Maiduguri da kewaye, yana mai zargin wasu jami’an tsaro da hannu a yaduwar laifuka da dabi’un banza a tsakanin al’umma.
Farfesa Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin kaddamar da kwamitin da aka sake wa fasali domin rushe otal-otal da gidajen karuwai da maboyar ’yan daba da masu aikata laifuka a fadar gwamnatin jihar da ke Maiduguri.
A cewar gwamnan, wasu tsofaffi da ma’aikatan jami’an tsaron da ke aiki a yanzu sun taka rawa matuka wajen jefa matasa cikin ayyukan laifi, irin su ta’addanci, karuwanci, shaye-shaye da kuma dabanci.
Gwamna Zulum ya ce yawaitar sayar da giya da kayan maye na kara haddasa rikici tsakanin kungiyoyin masu tayar da hankali, kawalci, da kuma satar mutane, wanda hakan ke kara barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.