Attajirin nan na duniya Bill Gates, ya bayyana aniyarsa ta raba kaso 99% na dukiyar da ya mallaka da ta kai Dala bilyan 200, ga al’ummar duniya. Bill Gates ya kuma ayyana kudirinsa na rufe Gidauniyar Bill and Melinda Gates.
Wanda ya kafa kamfanin Microsoft, Bill Gates ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a shafin rubuce-rubucensa na intanet, Gates Notes, inda ya ce gidauniyar wadda ke daga cikin manyan kungiyoyin agaji a duniya, za ta daina aiki kafin ranar 31 ga Disamba, 2045.
Jaridar Daily Mail ta rawaito cewa watakila ragowar kaso daya na 1% na dukiyar za ta tafi ga ‘ya’yansa uku da suka hada da Phoebe, Rory, da Jennifer.