Robert Francis Prevost, dan asalin birnin Chicago a Amurka, an haife shi a ranar 14 ga Satumba, 1955, yana da shekaru 69 a yanzu.
An nada shi a matsayin sabon shugaban Ma’aikatar Bishop-Bishop da kuma Shugaban Hukumar Paparoma kan Latin America a cocin Katolika.
Prevost, wanda memba ne na Darikar Saint Augustine, ya shafe shekaru da dama yana aikin mishan a Peru, inda ya rike mukamai daban-daban kafin daga bisani ya zama bishop na Chiclayo.
A shekarar 2023, Paparoma Francis ya nada shi Kardinal, sannan daga baya ya dora masa nauyin jagorantar daya daga cikin manyan ma’aikatun cocin Katolika a Vatican, yanzu kuma ya zama sabon Fafaroma bayan rasuwar Fafaroma Francis wanda za’a rinka kiransa Fafaroma Leo na 14.