Faduwar darajar Naira ta ci gaba a Larabar makon nan yayin da Nairar ta kara raunana a kasuwar canji, inda aka tashi a daren Larabar da farashin N1608 kan kowace Dala daya.
A ranar Talata, Naira ta fadi da N1 inda aka rufe kasuwar canji da farashin N1606.64 kan Dala daya a kasuwar musayar kudade ta Nijeriya.
A cewar bayanan da babban bankin CBN ya fitar, Naira ta fadi da kusan N3 a kan kowace Dala daya a ranar Litinin, inda aka rufe kasuwar canjin da farashin N1605.62 daga N1602.18 a ranar Juma’a.