Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya bayyana dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Agbebaku, tare da wasu ‘yan majalisa biyu — Hon. Sunday Fada Eigbiremonlen da Hon. Idaiye Yekini Oisayemoje — sun sanar da sauya shekar su zuwa jam’iyyar APC a ranar Talata.
A yayin da yake sanar da wannan mataki a zauren majalisar a ranar Laraba, Agbebaku ya ce sauya shekar tasa ya samo asali ne daga niyyarsa ta ci gaba da rike kujerar shugaban majalisa domin amfanin mazabarsa.
Shugaban majalisar ya jaddada cewa sauya shekar ba don wani amfani na kai ba ne, illa dai kishin ci gaban al’umma da yankin da ya fito.