‘Yan sanda a jihar Ondo sun tabbatar da cafke wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin Basaraken gargajiya, Adekolajo Aladeseyi, bisa zargin nada kansa a matsayin Olujare na Ijare da ke karamar hukumar Ifedore ta jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya rawaito cewa an kama karin wasu mutane hudu da ake zargin sun taimaka masa wajen gudanar da nadin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Olutokunbo Afolabi, yayin da yake tabbatar da kama Aladeseyi, ya ce an cafke shi ne bisa umurnin gwamnatin jihar.