A wani sakon tunatarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook albarkacin ranar Juma’a, hukumar da ke yaĆ™i da cin hanci da rashawa a Najeriya, wato EFCC, ta bayyana cewa cin hanci wata la’ana ce da ke lalata al’umma, tana mai kira ga ‘yan Najeriya da su tsabtace kansu daga wannan mummunar dabi’a.
EFCC ta ambaci wani hadisi daga cikin Sahih Hadith ɗin Abu Dawud mai lamba ta 3580, inda Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah ya la’anci mai bayar da cin hanci da wanda aka baiwa.”
Hukumar ta ce, kowane ɗan ƙasa na da rawar da zai taka wajen yaƙar cin hanci da gina ƙasa mai gaskiya da adalci.