Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya haramta sayar da mai a gidajen mai a karamar hukumar Bama da Banki.
Karamar hukumar Bama na a yankin arewa maso gabashin jihar Borno, kuma tana da iyaka da kasar Chadi sannan tana da iyaka da kasar Kamaru.
Umurnin ya biyo bayan tattaunawa tare da tuntubar hukumomin tsaro a jihar, da nufin magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce matakin na daga cikin dabarun da gwamnati ta dauka na dakile ayyukan tada kayar baya.