Shugabannin biyu sun tattauna a yayin bikin nasarar da Rasha ta samu a yakin duniya na biyu da ya gudana kasar Rasha, inda suka jaddada aniyarsu ta karfafa hadin gwiwa a harkokin siyasa da tattalin arzikin kashashen.
Putin ya yaba wa Masar a matsayin babbar abokiyar huldar kasar Rasha a Afirka kuma ya bayyana dangantakar kasashen biyu a matsayin mai dumbin tarihi.
Shugabannin biyu sun yi bayyana fatan samun nasara a taron majalisar kasashen biyu na Masar da Rasha da aka shirya gudanarwa tsakanin 12-14 ga watan Mayu mai zuwa.