Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi wa fursunonin afuwa ne a lokacin da ya kai ziyarar ba zata a gidan gyaran hali, tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa makasudin ziyarar shi ne duba halin da fursunonin ke ciki da kuma lalubo hanyoyin da gwamnatin jihar za ta tallafa wa jin dadinsu.
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yawan fursunonin da ke jiran shari’a, inda ya ce daga cikin fursunoni 1,939, mutum 382 ne kawai aka yanke musu hukunci, yayin da 1,536 ke jiran shari’a.
Ya kuma ba da tabbacin cewa jihar za ta hada kai da bangaren shari’a domin a gaggauta yi musu da kuma rage cunkoso a gidan gyaran halin.