Daraktan kungiyar Al Nassr, Fernando Hierro, ya bayyana cewa har yanzu suna ci gaba da tattaunawa da Cristiano Ronaldo kan yiwuwar ci gaba da zaman sa a kulob din.
Ya jaddada cewa Ronaldo ya taka muhimmiyar rawa a kungiyar, tare da inganta martabarta a idon duniya, yana kuma fatan a cimma matsaya don ci gaba da kasancewarsa a Al Nassr.