Wata kungiya mai suna Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners (ALDRAP) ta shigar da kara a gaban Kotun Kare Hakkin Masu Sayayya, tana neman tilasta wa sanatocin Najeriya mayar da wani kaso mai yawa na albashinsu tun daga 2023, bisa zargin rashin tabuka abin kirki a majalisa.
Kungiyar a cewaar rahoton da jaridar Punch ta fitar tana neman a karbo cikakken albashin sanatoci 40 da suka rike kujeru a Majalisar Dattawa da kuma Majalisun ECOWAS da Afirka, wanda suka yi rufa-rufa a aiyukan mazabunsu.
A cewar sanarwar da sakataren gudanarwa na ALDRAP, Amuga Williams, ya aika wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio a ranar 26 ga Mayu, hakkin ‘yan Nijeriya ne su ci gajiyar ayyukan mazabu daga majalissa, kuma sun dauki matakin ne a madadinsu.