Rundunar Operation Hadin Kai ta kama sojoji 18 da ‘yan sanda 15 bisa zargin sayar da makamai ga ‘yan ta’adda a wani samame da aka gudanar a jihohi 11 karkashin shirin Operation Snowball.
Jaridar Punch ta ruwaito kakakin rundunar, Manjo Ademola Owolana, ya ce an kama su ne a Bauchi, Benue, Borno, Ebonyi, Enugu, Lagos, Plateau, Kaduna, Rivers, Taraba da Abuja.
Haka kuma an damke fararen hula 8 da wani basarake, ciki har da Ameh Raphael, wanda ake zargin da safarar makamai tun 2018, inda aka gano N45m a asusunsa.