Kasar Faransa za ta hana shan taba a wuraren da yara ke zama da cikin jama’a, daga ranar 1 ga Yuli, 2025.
Wuraren da za’a hana sun hada da bakin teku, wuraren shakatawa, hanyoyin shiga makaranta, da wuraren wasanni.
Ministar lafiya, Catherine Vautrin, ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 29 ga Mayu,inda ta bayyana cewa dole ne a daina shan taba musamman a wuraren da yara ke zuwa.