Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, yayin rantsar da sabbin kwamishinonin zabe guda shida da majalisar dokoki ta kasa ta amince da su kwanan nan.
A cewarsa, za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti a ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026. Za a fara zaben fidda gwanin ‘yan takara na jam’iyyun siyasa daga ranar 20 ga Oktoba, 2025, sannan a kammala ranar 10 ga Nuwamba, 2025.
Hakanan, jam’iyyu za su rufe shigar da fom din ‘yan takara da yammacin ranar 22 ga Disamba, 2025.
A jihar Osun kuwa, za a gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.