Jihar Kano ta samu Naira biliyan 65 a matsayin kudaden shiga na cikin gida (IGR) a shekarar 2024, kuma ana sa ran adadin na iya karuwa zuwa tsakanin Naira biliyan 70 zuwa 75 bayan cikakken bincike.
A shekarar 2025, jihar na fatan samun kudaden shiga har zuwa Naira biliyan 200. Don cimma wannan buri, Hukumar Haraji ta Kano (KIRS) na shirin yin rajistar masu biyan haraji miliyan biyu, inda ake sa ran kowane mutum zai biya Naira 100,000 a shekara.
Haka kuma, KIRS ta bayyana ci gaba da take samu wajen bin ka’idojin biyan haraji da kuma amfani da sabon tsarin biyan haraji na lantarki, wanda aka haɗa da Lambar Shaida ta Kasa (NIN).