‘Yan wasan na kan hanyarsu ne ta dawowa gida Kano daga jihar Ogun, inda suka fafata a gasar ta kwallon kafa.
Jaridar Daily Nigerian ta ce cikin wadanda hatsarin ya yi ajalinsu akwai ‘yan wasa 17 da mai magana da yawun hukumar wasanni ta jihar Kano Galadima Ibrahim da sauran wasu jami’ai.
Kawo yanzu wadanda suka ji raunuka na samun kulawar likita.