Gwamnatin tarayya ta gargadi dillalin motoci a Abuja, wanda aka fi sani da Alamin Sarkin Mota, kan yi wa ma’aikatan gwamnati ba’a a cikin bidiyon talla da yake yi.
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA ce ta yi wannan gargadi a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun babban daraktanta, Lanre Issa-Onilu, a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sarkin mota ya yi kaurin suna wajen bayyana cewa motocin da yake talla sun fi karfin ma’aikaci ya siya, saboda tsadarsu.
A saboda haka hukumar ta gargadi dillalin motocin da ya kiyaye irin kalaman da yake yi a duk lokacin da yake kokarin tallata motocinsa domin kaucewa cutar da jajirtattun ma’aikatan Nijeriya.