Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Faransa, Kyllian Mbappe ya ce ko kadan bai yi bakin ciki da nasarar da tsohuwar kungiyarsa ta kwallon kafa PSG ta samu a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai wato Champion league ba.
Mbappe ya bayyana ma ‘yan jaridu gabanin wasan da za su buga a ranar Lahadi cewa, lokacin barinsa PSG ne ya yi ba wai ya yi gaggawar tafiya ba ne kuma ko kadan bai yi da-na-sani ba.
Nasarar PSG a Champions league ba tare da ni ba sam bai dame ni ba, ina murna da hakan don ina ganin sun cancanta.
Mbappe, mai shekaru 26 ya sauya sheka daga PSG zuwa Real Madrid a 2024 cike da fatar cin kofin Champions league, sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon fitar da su da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi a watan Afrilu.
Idan ba a manta ba, PSG ta lallasa Inter Milan da ci 5-0 a wasan karshe na Champions league wanda shi ne Karin farko da kungiyar PSG ta ci kofin.