Kungiyar al’adu da ci-gaban kabilar Eggon, ta koka game da mummuna harin da ya kai ga rasa ran daya daga cikinsu wato, ASP Baba Mohammed, DPO din Rano.
Mohammed, dan asalin jihar Nasarawa, shi ne wanda wasu matasa suka far masa wanda hakan ya yi sanadiyar rasa ransa a Jihar Kano.
A cikin wani jawabi da kungiyar ta yi ma ‘yan jarida a garin Lafiya, Shugaban Kungiyar na kasa, Mandy Abuluya ya yi kira ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya da ta yi bincike don gano wadanda suka aikata wannan barnar tare da hukunta su.
Mandy ya jajanta ma iyalan mamacin, da kuma kabilar Eggon, gwamnatin jihar da Shugaban ‘yan sandan Nijeriya game da lamarin.