Jam’iyyar PDP ta ce ta kammala shirin sauya fasalin shugabancinta na jihohi da kuma yankin Kudu maso Kudu, a wani yunkuri na kawar da ‘ya’yanta marasa biyayya da kuma dakile sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu.
Wani mamba na Kwamitin gudanarwa na kasa NWC na jam’iyyar PDP, wanda ya yi magana da jaridar PUNCH da bai so a ambaci sunansa ba, ya ce wannan sauyi na daga cikin sabbin matakan da jam’iyyar ke dauka don sake farfado da kanta gabanin zaben shekarar 2027.
A cewarsa, jam’iyyar ba ta gamsu da yadda ake ta sauya sheka ba a ‘yan makonnin nan, kuma yanzu ta shirya daukar mataki mai karfi.