Hukumar kula da gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta bayyana cewa kusan dukkan fursunonin kasar yanzu sun shiga cikin bayanan hukumar NIMC.
Mai magana da yawun hukumar, DC Umar Abubakar, a wani rahoton jaridar Daily Trust ya ce fursunoni 59,786 daga cikin 80,879, wanda ya kai kashi 74%, aka riga aka yi wa katin dan kasa ta hukumar NIMC.
Ya ce hakan ya samu ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa NCoS da hukumar katin dan kasa ta NIMC.