Kungiyar ‘Yan Kasuwar Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta bukaci Kamfanin Dangote da ya rage farashin man fetur daga N825 zuwa kasa da N800 a lita.
Jaridar Punch ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce Dangote na da dukkan ababen da za su sa a sayar da man a farashi mai sauki.
Wannan na zuwa ne bayan da Aliko Dangote ya bayyana cewa farashin man a Najeriya ya fi na yawancin kasashen Yammacin Afirka arha da kashi 55%.