Sanata Ali Ndume na Borno ta Kudu ya bayyana cewa bai goyi bayan matakin gwamnonin APC 22 da suka marawa Shugaba Bola Tinubu baya na yin tazarce a takara a 2027 ba.
A wata hira da Channels TV, Ndume ya ce halin da Najeriya ke ciki ya tabarbare, tare da karin matsin rayuwa da rashin tsaro.
Ya ce saboda rashin dacewar lamarin ne ya bar dakin taron a Fadar Shugaban Kasa lokacin da aka bayyana goyon bayan.