Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya ce shugaba Bola Tinubu ya fi abokan hamayyar sa da suke shirin yin hadaka wayo da lissafin siyasa.
Tsohon mai magana da yawun tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce ganawar da suka yi da shugaba Tinubu a baya-bayan nan ba ta da nufin cin amanar alakarsa da Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne.
Segun Sowunmi ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yake hira a gidan Talabijin na Channels, inda ya ce dama can baya sukar shugaba Tinubu dan haka duk tunanin da jama’a suke yi akansa ba haka bane.