Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta gayyaci mawakiya ‘yar asalin Nijeriya, Temilade Openiyi wadda aka fi sani da Tems, domin gudanar da wasa a gasar da za a fara ta FIFA Club World Cup karo na fatko, wanda zai gudana a filin wasa na MetLife da ke New York na kasar Amurka a ranar 13 ga Yuli.
Tems za ta hadu da mawaƙin Colombia J Balvin da tauraruwar Doja Cat domin gudanar da wasan a ranar wasan karshe na gasar.
A cewar wata sanarwa da Global Citizen ta fitar a shafinta na yanar gizo, wadanda suka shirya shirin, za a watsa shirye-shiryen ne kai tsaye da kuma gidan talabijin na DAZN.com, wanda zai bai wa magoya bayanta a duk fadin duniya damar kallon wasan.