Gamayyar kungiyoyin matasa a jihar Rivers sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dawo da mulkin dimokaradiyya a jihar tare da mayar da gwamna Siminalayi Fubara gabanin bikin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yuni.
Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Imeabe Oscar, shugaban kungiyar matasan Kudu-maso-Kudu na kasa wanda ya zama shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin matasan jihar Ribas ya aike wa manema labarai.
Kungiyoyin matasan cikin rahoton da jaridar Punch ta wallafa a ranar Talata, sun bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa Fubara barazana ce kai tsaye ga tsarin mulkin kasar da kuma barazana ga tushen dimokuradiyya a Nijeriya.