Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya sanar da bayar da tallafin a lokacin da ya jagoranci tawagar jihar a ziyarar jaje a gidan gwamnati dake Minna.
Ya ce an bayar da tallafin ne domin kara wa kokarin gwamnatin jihar Neja wajen magance kalubalen da aka fuskanta.
Da yake jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Neja, Farfesa Zulum ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata gwamnatocin kasashen duniya su hada karfi da karfe domin dakile illolin sauyin yanayi a cikin al’umma.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da ingantaccen tsari wanda zai duba tare da magance matsalar sauyin yanayi a fadin kasar.