Gwamnatin jihar Bauchi karkashin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ta gayyaci al’umma a fadin jihar da su mika takardar neman kafa sabbin masarautu da gundumomi a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, ranar Litinin.
A halin yanzu dai jihar Bauchi tana da masarautu shida da suka hada da Bauchi, Katagum, Misau, Jama’are, Ningi da Dass.
Ko a watan Disamba 2024 gwamna Bala Abdulkadir ya amince da kafa masarautar Seyawa mai hedikwata a karamar hukumar Tafawa Balewa.
Solacebase ta rawaito cewa Muhammed ya bayyana hakan na daya daga cikin kokarin gwamnatin sa na ganin an samar da mafita ga matsalolin da suka dabaibaye na yunkurin samar da masarautar Seyawa, wanda ya gurgunta kokarin gwamnatocin da suka shude sama da shekaru talatin.