Wani sabon bincike da cibiyar bincike ta CJID ta gudanar a jihar Rivers, yawancin mutane sun nuna rashin amincewarsu da ayyana dokar ta baci da gwamnatin tarayya ta yi a jihar ta Rivers.
Binciken da aka yi a bangarori daban-daban da suka hada da matasa, mata, ma’aikatan gwamnati, ‘yan kasuwa, da mazauna kauyuka da birane, ya nuna cewa kashi 68.2 na mazauna jihar ta Rivers ba su amince da dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kakaba a ranar 18 ga Maris, 2025.